Gwamnatin Najeriya na son kashe mahaifi na - Diyar El-Zakzaky

Gwamnatin Najeriya na son kashe mahaifi na - Diyar El-Zakzaky

Badia Ibrahim El-Zakzaky, diyar jagoran kungiyar IMN, Ibrahim Zakzaky ta bayyana matukar damuwarta kan halin da lafiyar mahaifinta ke ciki bayan an mayar da shi gidan yari.

Badia ta shaidawa kafanin dillancin labarai na AhlulBayt a ranar Laraba cewa, "makonni uku da suka wuce, gwamnatin Najeriya sun mayar da Sheikh Zakzaky gidan yari duk da cewa ba shi da cikaken lafiya kuma ba su bar shi ya karbi maganinsa ba ko ganawa da likitocinsa.

"Niyyar su shine su kashe Sheikh Zakzaky kuma suna fitinar iyalan mu sosai", kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Tun a shekarar 2015, Jami'an tsaro na Najeriya sun kai sumame a Zaria inda suka kama Zakzaky suka tsare shi.

An kashe a kalla mutane 300 cikin mabiyansa da yaransa uku yayin sumamen. Zakzaky ya rasa idonsa daya sannan matansa da samu munanan rauni.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Tun daga lokacin ya kasance a tsare a hannun hukuma tare da wasu da dama cikin mabiyansa.

A ranar 5 ga watan Disambar 2019 ne wata babbar kotu ta umurci Hukumar DSS ta mayar da malamin da matarsa, Zinat zuwa gidan gyaran hali a Kaduna.

'Yan kungiyar ta IMN sun nuna damuwarsu kan umurnin kotun inda suka ce idan ba asibiti aka kai malam da matarsa ba tabbas an jefa su cikin fitina ne.

IMN ta ce gidan gyaran halin na Kaduna ya lalace inda suka kara da cewa a nan ne wasu daga cikin wadanda aka kama yayin sumamen da aka kai a 2015 suka mutu saboda rashin kulawa.

A shekarar da ta gabata ne IMN ta zargi gwamnati da yunkurin kashe Zakzaky a gidan gyaran hali bayan an samu sinadarin lead da cadmium masu ila a jininsa.

A watan Augustan 2019, Dakta Pourrahim Najafabadi ya ce akwai bukatar kwararrun likitoci su duba Zakzaky a kasar waje domin babu irin asibitin da za ta bashi kulawar da ya ke bukata a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel