Harin jirgin kasan Abuja: Karya ne, hakan bai faru ba - NRC ta yi martani

Harin jirgin kasan Abuja: Karya ne, hakan bai faru ba - NRC ta yi martani

Dirakta Manaja na hukumar jiragen kasan Najeriya NRC, Injiya Fidet Okhiria, ya karyata rahotannin cewa yan bindiga sun kaiwa jirgin Kaduna zuwa Abuja da safiyar yau Alhamis, 2 ga watan Juaniru, 2020. Daily Trust ta ruwaito.

Mista Okhiria wanda yayi martani a hirar wayar tarho da manema labarai inda ya jaddada cewa babu abinda ya faru ga jirgin kasa.

Ya kalubalanci wadanda ke yada jita-jitan cewa su ziyarci tashan jirgin domin ganin yadda abubuwa ke gudana.

Bugu da kari, Manajan gudanarwan tashan jirgin Abuja-Kaduna, Mista Victor Adamu, ya bayyanawa Daily Trust cewa bai samu rahoton wani hari ba kuma komai na cigaba da gudana yadda aka saba.

Hakazalika mai magana da yawun hukumar, Mahmood Yakub, ya bayyana cewa wasu yan bakin ciki ne ke yada jita-jita.

Yace: "Wannan labarin boge ne. Babu wanda ya kai jirgin NRC hari a hanyar Abuja/Kaduna."

"Wannan wani tuggu yan bakin ciki ke shiryawa domin koran mana fasinja. Mun dauki wannan matsayin wani kaidin bata mana suna."

Da safiyar Alhamis, Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu gungun yan bindiga sun bude ma jirgin kasa wuta a kan hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya Abuja daga jahar Kaduna amma babu wanda ya samu rauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel