Rusau: Ministar Buhari ta soki rushe gidan mahaifinta a Kwara

Rusau: Ministar Buhari ta soki rushe gidan mahaifinta a Kwara

Karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki, ta nuna rashin jin dadinta a kan rushe gidan mahaifinsu da gwamnatin jihar Kwara tayi a sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Idan zamu tuna, gwamnatin Gwamna AbdulRazaq ta yi ikirarin cewa kadarar bata da takardu, kuma ba a biya ko sisin kwabo ga gwamnatin jihar ba kafin mahaifin Sarakin ya amshi filin.

A safiyar yau ne wajen karfe 4 na asuba aka gano cewa jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda suka hada da mata tsoffi a yayin da suke rushe gidan.

Amma kuma, a martanin gaggawa na ministar, ta koka cewa gwamnan yayi yunkurin shafe tarihinsu ne: "Muna da tarihi kuma muna alfahari da shi".

A takardar da mataimakiyarta ta musamman, Titilope Anifowoshe ta fitar a ranar Talata, ta kira wannan kungiyar da 'GRS-OLOYE' don yi wa iyalan Sarakin kara.

DUBA WANNAN: Kannywood: Manyan nasarori 5 da masana'antar ta samu a 2019

Ministar ta ce, "Abubuwa da yawa sun faru a wannan shekarar, a takaice har da sa'o'in karshe na shekarar 2019. Amma zamu cigaba da jarumta tare da yakini a duk matakin da zamu dauka.

"Zamu cigaba da tafiya a daidaice duk da bamu san abinda zai faru ba nan gaba. Suna tsarawa kuma Allah na tsarawa, amma tsarin Allah shine na gaskiya.

"Muna da tarihi kuma muna alfahari da shi. Muna fatan Allah ya yafe mana zunubbanmu tare da na wadanda suka riga mu gidan gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: