Siyasa rigar yanci: Dan majalisa ya baiwa mutane 220 mukamin masu bashi shawara

Siyasa rigar yanci: Dan majalisa ya baiwa mutane 220 mukamin masu bashi shawara

Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Akoko ta Arewa maso gabas da Akoko ta Arewa maso yamma a majalisar wakilan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya dauki mutane 220 aiki a matsayin hadimansa da zasu taya shi aiki.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito mai magana da yawun dan majalisan, Alao Babatunde ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba inda yace Olubunmi ya nada shugaban ma’aikatansa guda 1, mashawarta na musamman guda 6, mataimaka na musamman guda 156 da kuma hadimai 67.

KU KARANTA: Jami’an hukumar kashe gobara ta Kano ta tseratar da mutane 11 da dukiyar naira miliyan 33

Babatunde yace nadin mukaman ya karade dukkanin mazabu 23 dake cikin kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso gabas da Akoko ta Arewa maso yamma da yake wakilta a majalisar wakilan Najeriya.

Haka zalika, Mista Tunji, wanda yake jagorantar kwamitin majalisar wakilai dake kula da hukumar cigaban Neja Delta, ya nada har da mutane daga jahohin dake da arzikin man fetir.

“A kokari na bauta ma jama’ar mazaba nan a Akoko ta Arewa maso gabas da Akoko ta Arewa maso yamma, ina sanar da nadin sabbin hadimai na, na zabo wadannan mutane ne sakamakon jajircewarsu da kuma sadaukarwa wajen kyautata rayuwar jama’an yankin.” Inji shi.

A wani labarin kuma, A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun bude ma jirgin kasa wuta a kan hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya Abuja daga jahar Kaduna.

Jirgin ya tashi daga tashar jirgin kasa dake garin Rigasa na jahar Kaduna da misalin karfe 10 na safe, sai dai bai yi nisa ba ya ci karo da yan bindiga a daidai garin Katari, kimanin kilomita 70 kafin shiga Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel