Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan ta'adda Boko Haram 76, sun ceto mata da yara 161

Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan ta'adda Boko Haram 76, sun ceto mata da yara 161

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun hallaka yan ta'addan Boko Haram da daular Musulunci a yankin Afrika ta yamma ISWAP kuma sun ceto mata da yara a jihar Borno.

Jami'in yada labarai na hukumar, Kanar Aminu Iliyasu, a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Abuja ya ce an gudanar da farmakin ne da hadin gwiwan rundunar sojin kasa da kasa Multinational Joint Task Force (MNJT).

Iliyasu ya ce Sojin da aka tura Bama sun hallaka dan ta'adda daya kuma sun damke daya da rai. Sun ceto mata takwas da yara shida a kauyun Tafana 1, 2 da 3 a Bama ranar 27 ga watan Disamba, 2019.

Ya kara da cewa kai tsaye aka baiwa yaran rigakafin shan inna.

A cewarsa, Sojin sun kwace tutar Boko Haram, kwari da gwafa 16, harsasan 7.62mm talatin.

Bugu da kari, Iliyasu ya bayyana cewa dakarun Sakta 3 tare da hadin gwiwan MNJTF sun ragargaza motocin yan Boko Haram 15 a Arewacin Borno.

Ya ce Sojin sun damke yan Boko Haram 75 kuma sun ceto maza 79 da mata 68 daga hannun yan ta'addan.

A cewarsa, Sojin sun mika wadanda suka ceto ga ma'aikatan bayar da agajin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel