Ban damfari ASD $20,000 ba - Shehu Sani ya bayyanawa EFCC

Ban damfari ASD $20,000 ba - Shehu Sani ya bayyanawa EFCC

Sanata Shehu Sani ya bayyanawa jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC cewa bai nemi $20,000 (milyan bakwai) wajen dan kasuwa, Alhaji Sani Dauda ASD ba. The Nation ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a shirye yake da yayi ido hudu da ASD domin wanke kansa daga zargin damfara.

Hukumar EFCC data damke Shehu Sani, ta bayyana cewa Alhaji Sani Dauda ne ya kawo kararsa.

Ana sa ran ASD zai bayyana gaban EFCC yau (Alhamis) domin amsa tambayoyi da kuma ido hudu da Sanata Shehu Sani.

An samu labarin cewa Sanatan ya musanya zargin da ake masa a jawabin da ya rubuta a hedkwatan EFCC.

Wani majiya mai karfi da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa The Nation cewa: "Lokacin da muke yiwa Shehu Sani tambayoyi, ya ce bai karbi $20,000 daga hannun shugaban kamfanin ASD Motors, Alhaji Sani Dauda, ba."

"Ya kara da cewa tun da shi ba ma'aikacin EFCC bane, ta yaya zai bukaci kudi daga hannun Dauda a madadin shugaban EFCC, Ibrahim Magu."

"Duk da cewa ya yi na'am da sanin Alhaji Sani Dauda kuma ya jajinta masa kan abinda ya faru a Nuwamban 2019, ya lashi takobin wanke kansa a gaban EFCC da kotu."

"Masu bincike zasu tattauna da ASD da Shehu Sani ranar Alhamis. Mun bukaceshi ya kawo dukkan takardun kafa hujja."

"Hakazalika muna bincike kan sakonnin wayan da sukayi tsakanin Sanatan da ASD. Da alamun akwai tanakudi."

Bugu da kari, mun samu labarin cewa EFCC za ta gayyaci yan kasuwan canjin da akayi harkan da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel