Da duminsa: NAF ta yi wa manyan dakarunta 76 canjin wuraren aiki

Da duminsa: NAF ta yi wa manyan dakarunta 76 canjin wuraren aiki

Rundunar sojin saman Najeriya a ranar Laraba ta bayyana sauyin wajen aiki da tayi wa Air Vice Marshals 36 da Air Commodore 40.

Rundunar sojin saman ta sanar da hakan ne ta bakin kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce wannan canjin ya biyo bayan karin girman da aka yi wa wasu hafsoshin sojin ne tare da murabus da wasu suka yi.

Rundunar sojin saman ta bayyana cewa, wannan canjin anyi shi ne don assasawa tare da tabbatar da ingancin aiyukansu.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Ibikunle ya ce, "shuwagabannin bangaren da sauyin wajen aikin ya shafa sun hada da AVM Oladayo Amao, tsohon shugaban horarwa da aiyuka, wanda a halin yanzu aka mayar shugaban dokoki da tsari. An nada James Gwani a matsayin sabon CTOP."

Ya kara da cewa, "AVM Musibau Olatunji an nada shi a matsayin shugaban fannin kere-kere na jiragen sama, AVM Mohammed Idris kuwa ya zama babban hafsi a fannin shugabanci. AVM Abubakar Liman, wanda a da shine shugaban cibiyar natsarwa ta sojin saman na jihar Legas, an nada shi yanzu a matsayin shugaban kwalejin ma'aikatar da ke Jaji, jihar Kaduna."

Ya kara da cewa, AVM Kingsley Lar an nada shi a matsayin shugaban AFRC da ke Oshodi, jihar Legas, yayin da AVM Abdulganiyu Olabisi ya koma cibiyar fasaha ta sojin sama dake jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel