NAPTIP ta kai sumame gidan marayu a Kaduna, ta kwashe yara ta tafi da su Kano

NAPTIP ta kai sumame gidan marayu a Kaduna, ta kwashe yara ta tafi da su Kano

An shiga rudani a gidan marayu na Du Merci da ke unguwar Narayi a Kaduna a karamar hukumar Chikun yayin da jami'an Hukumar kana fataucin mutane (NAPTIP) suka kai sumame gidan suka kwashe marayun.

Daily Trust ta ruwaito cewa jamian na NAPTIP sun kai isa gidan ne tare da jamian yan sanda daga rundunar ta Kano tare kuma da daya daga cikin wadanda suka kafa gidan marayun, Mista Solomon Tarfa.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin da mai'aikatan gidan ke shirin bikin sabuwar shekara.

'Yar uwar daya daga cikin wadanda suka kafa gidan, Misis Maria Phil Ariyo ta tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin inda ta ce 'yan sanda daga jihar Kano sun kwashe marayun.

Ta ce, "Bayannan da na samu sun ce yaran sun kwana ne a ofishin 'yan sanda sannan daga baya aka tafi da su gidan marayu da ke Nasarawa a jihar Kano.

"Muna sauraron 'yan sanda su fada mana dalilin da yasa suka kwashe yaran kuma suka kama wadanda suka kafa gidan marayun."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Ta yi bayyanin cewa gidan marayun yana da rajistan CAC kuma ya kai kimanin shekaru 30 da kafuwa.

A cewarta, hedkwatan gidan marayun yana Kano kuma dukkan yaran da ke gidan an tsinto su ne a titi ko kuma daga asibiti.

Da aka tuntube ta, Kwamishinan Cigaban Al'umma, Hafsat Baba ta ce ma'aikatanta da san da batun sumamen da NAPTIP reshen jihar Kano ta yi.

Ta ce, "Mun san da sumamen don NAPTIP na jihar Kano ta rubutowa ma'aikatar mu wasika inda ta nemi sanin ko sun san da zaman gidan marayun kuma binciken da NSCDC ta yi ya nuna cewa ba su taba yin rajista da gwamnatin jiha ba.

"Saboda haka, a wurin mu ba su da ikon cigaba da tafiyar da gidan saboda ba suyi rajista da ma'aikata ba kuma ba su cikin kungiyar gidajen marayu da gwamnati ta san da zaman su a jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel