An kaiwa Gwamna Oyetola da matarsa hari a taron murnar sabon shekara

An kaiwa Gwamna Oyetola da matarsa hari a taron murnar sabon shekara

- Wasu bata gari sun kai wa hari gwamnan jihar Ogun da tawagarsa a jajiberin sabuwar shekara

- Bata garin sun jefi gwamnan ne, matarsa da shugaban ma'aikatan jihar a filin wasa na Nelson Mandela da ke Osogbo

- A halin yanzu dai mutum daya ya shiga hannu, baya da aka gane yana da sa hannu a cikin wannan tada zaune tsayen

Wasu bata gari sun kaiwa gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da wasu mukarrabansa hari a sa’o’in farko na ranar Laraba a yayin taron fara murnar sabuwar shekara a gidan gwamnatin jihar dake Osogbo.

Wannan taron da aka fara a filin yanci na Nelson Mandela ya tashi ne babu dadi wajen karfe 1 na dare, yayin da wasu mutane suka fara jifan ida manyan bakin, gwamnan, matarsa da shugaban ma’aikatan jihar ke zaune kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Wani mutum daya da ba a tabbatar da sunansa ba a yayin rubuta wannan rahoton, ya shiga hannu saboda an gano yana da hannu a cikin wannan tashin-tashinar da karantsaye ga zaman lafiya.

Daga cikin manyan bakin dake wajen akwai shugaban jam’iyyar APC na jihar, Gboyega Famoodun; sakataren gwamnatin jihar, Wole Oyebamiji; da kwamishinan aiyuka na musamman, Lekan Badmus.

Kafin faruwar al’amarin, an saka kida na wakokin zamani kuma mawakan zamanin suna ta baje kolinsu da nuna bajintarsu a fili. Ana kuma bada kyautuka ga mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel