Ganduje ya fara biyan mafi karancin albashi N30,600

Ganduje ya fara biyan mafi karancin albashi N30,600

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da biyan mafi karancin albashin N30,600 ga ma'aikatan jihar a watan Disamban 2019.

Kwamishanan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki.

Garba ya bayyana cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniya da kungiyar kwadago, gwamnatin gwamna Abdullahi Ganduje ta alanta niyyar biyan mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Garba ya kara da cewa bisa ga yarjejeniyar da akayi tsakanin gwamnatin jihar da kwamitin yarjejeniya, za'a biya bashin karin daga watan Afrilu zuwa Nuwamban 2019 kada-kadan.

Kwamishanan ya yi kira ga ma'aikatan jihar su mayar da alkhairin nan ta hanyar nuna kwazo wajen aikinsu.

Hakazalika ya yi kira da ma'aikatan amsan haraji su zange dantse wajen samarwa gwamnatin jihar kudi ta hanyar tabbatar da cewa masu kudi da kamfanoni suna biyan harajinsu saboda a yiwa al'ummar jihar ayyukan cigaba.

KARANTA: Yunkurin tsige shugaban jam'iyya: Ko a jikina - Oshiomole

A jihar Bauchi kuwa, gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya amince da biyan ma'aikata a jihar karancin albashi na N30,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga Mohammed Baba, sakataren gwamnatin jihar zuwa ga manema labarai a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, a Bauchi.

A cewar jawabin, sabon umurnin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, daga ranar 1 ga watan Janairu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel