Yunkurin tsige shugaban jam'iyya: Ko a jikina - Oshiomole

Yunkurin tsige shugaban jam'iyya: Ko a jikina - Oshiomole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomhole, a ranar Talata ya bayyana cewa bai damu da kokarin tunbukeshi daga kujerarsa da wasu gwamnoni ke shirin yi ba.

Oshiomole, wanda ke fuskantar barazana daga wasu gwamnoni karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa wajen ciyar da jam'iyyar gaba ba.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga 'yayan jam'iyya a kauyensa, Iyamho, jihar Edo.

Oshiomole ya yi kira ga masoyansa su cigaba da goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Yace: "Na zama shugaban jam'iyya ranar 24 ga Yuni, 2018 kuma muka samu nasarar farko a zaben jihar Ekiti."

"Da ikon Allah, muka sake samun nasara a zaben gwamnan jihar Osun."

"Daga nan kuma akayi zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya, kuma da ikon Allah muka samu nasara."

"Hakazalika muka samu rinjaye a majalisar dattawa da majalisar wakilai."

"Sabanin kuren da mukayi a 2015, mun gudanar da zaben shugabannin majalisa cikin lumana kuma jam'iyyarmu ta samu nasara a dukkan kujerun da akayi takara.

"Sannan muka je jihar Kogi muka samu nasara. Muka garzaya can kudu, Bayelsa."

"Saboda haka ina alfaharin cewa karkashin jagoranci na, mun samu jihar Kudu maso kudu daya."

DUBA NAN: Kimanin Jarirai 26,039 za'a haifa yau, ranar sabuwar shekara a Najeriya - UNICEF

Mun kawo muku rahoton cewa tuggun kokarin tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na cigaba da bunkasa amma da alamun gwamnonin dake goyon bayansa sun fi yan adawarsa yawa.

Gwamnonin dake kira ga cire Oshiomole na ikirarin cewa shi ya sababbawa jam'iyyar asarar wasu jihohi a zaben 2019 da jam'iyyar PDP ta samu a banza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel