Yarinya 'yar shekara 13 ta mutu a lokacin da take haifewa mahaifinta cikin shegen da ya dirka mata

Yarinya 'yar shekara 13 ta mutu a lokacin da take haifewa mahaifinta cikin shegen da ya dirka mata

- Luana yarinya ce mai shekaru 13 da ta rasa ranta wajen nakudar haihuwar cikin da mahaifinta ya dirka mata

- An zargi Tome Faba da fara lalata da 'yarshi tun tana da shekaru 9 a duniya, inda ya dura mata ciki lokacin da take da shekaru 13

- Ta rasu ne bayan an gano ta samu ciwon hanta, zubar jini yayin nakuda da karantar jini yayin nakuda

Wata yarinya mai shekaru 13 ta rasa ranta wajen haihuwa bayan da ta dau shekaru hudu mahaifinta na lalata da ita.

Jami'an 'yan sanda a kasar Brazil sun tabbatar da mutuwar Luana Ketlen a ranar 11 ga watan Disamba bayan da aka kwantar da ita a asibiti sakamakon ciwon cikin da ya addabeta. Binciken likitoci ne ya bayyana cewa ciki gareta.

An sanya wa Luana ruwan nakuda ta yadda likitoci zasu taimaka mata wajen haihuwar yaron da bai gama kwari ba. Cikin ikon Ubangiji sai yaron ya fito da rai amma mahaifiyar ta zubar da jini mai yawa da yayi ajalinta. An gano cutar hanta, ruwa a cikin huhunta da jinin jikinta da yayi kasa kafin rasuwarta.

Daga bisani ne 'yan sanda suka bada damar cafko mahaifinta mai suna Tome Faba mai shekaru 36 a duniya, Inda ake tuhumarshi da laifin cin zarafin 'yar shi tun tana shekaru tara da haihuwa.

Da farko Tome Faba yayi yunkurin tserewa amma sai aka kama shi a birnin Coari bayan mako daya.

KU KARANTA: Tirkashi: An dakatar da daurin aure a Jigawa bayan an gano cewa angon yana dauke da cutar kanjamau

Tome ya fara bayyana a gaban kotu ne a ranar 27 ga watan Disamba inda aka tuhumeshi da laifin cin zarafi da kuma kisan kai.

Kamar yadda Jose Barradas ya bayyana wa taron manema labarai, "Yarinyar bata san tana da juna biyu ba sai a watanni biyu da suka gabata. Tsananin ciwon ciki ne yasa likitoci suka gano tana dauke da cikin watanni biyar. Luana tace sun je kamun kifi ne da mahaifinta inda yayi mata fyade."

'Yan sanda sun gano cewa, Faba yayi barazanar halaka Luana matukar ta kai rahoton abinda ke faruwa. Dangi ne suka kaiwa jami'an 'yan sanda rahoto amma kafin a cafko shi sai yarinyar ta mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel