Mutane 525 muka ceto daga hannun yan bindiga - Gwamnatin jihar Zamfara

Mutane 525 muka ceto daga hannun yan bindiga - Gwamnatin jihar Zamfara

Jimillar mutane 525 suka tsirata daga hannun yan bindiga a jihar Zamfara, kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran, ya laburta.

Dauran ya bayyana hakan ne a Gusau ranar Talata yayinda yan jarida suka kai masa ziyarar taya murna a ofishinsa.

Ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane daga hannun yan bindiga ne sakamakon shirin Sulhu da zaman lafiya da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kaddamar watanni biyar da suka gabata.

Yace: "Wannan shirin sulhun ya taimakawa mutane 525 wajen komawa wurin iyalansu a watanni biyar da suka gabata."

"Hakan ya yiwu ne sakamakon shirye-shiryen gwamnatin Matawalle na tabbatar da tsaro kuma wasu jihohi na zuwa wajen Matawalle domin neman ilimin magance lamuran tsaro a jihohinsu."

Kwamishanan ya ce har yanzu ana cigaba da tattaunawa da yan bindiga domin ganin yadda zasu ajiye makamansu.

DUBA NAN: Dadiyata ba ya hannunmu - Kakin DSS ya nisanta hukumar daga zarge-zarge

Yace: "Akan wannan, muna tattaunawa da tsaffin shugabannin yan bindigan da suka rungumi zaman lafiya kuma muna amfani da hukumomin tsaron wajen dakile hanyoyin da yan bindigan ke samun makamai."

"A matsayina na shugaban kwamitin kwace makamai, mun gano cewa wasu makamn da yan ta'addan ke amfani da su sunfi na jami'an tsaronmu kyau da hadari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel