Dadiyata ba ya hannunmu - Kakin DSS ya nisanta hukumar daga zarge-zarge

Dadiyata ba ya hannunmu - Kakin DSS ya nisanta hukumar daga zarge-zarge

Hukumar tsaron farin kaya DSS ta fito ta bayyana cewa shararren matashin Kwankwasiyya kuma malamin jami'a, Abubakar Idris Dadiyata, ba ya hannunta.

Dadiyata, wanda ya kasance shararren dan adawan gwamnatin APC ya bace ne tun watan Agusta, 2019. Rahotanni sun bayyana cewa anyi awon gaba da shi ne yayinda yake tafiya gidansa dake Kaduna.

Mutane da dama sun zargi hukumar DSS da tsareshi amma a ranar Talata, kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya ce hukumar bata san inda Dadiyata yake ba.

Yace: "Mun samu labarin zarge-zarge a shafukan ra'ayi da sada zumunta cewa hukumarmu na tsare da wasu yan Najeriya musamman Abubakar Idris Dadiyata da Agba Jalingo."

"Maganar gaskiya itace wannan labari karya ne kuma anayi ne da gayya domin batawa hukumar suna a idon jama'a. Don an ce wasu yan bindiga sukayi awon gaba da Dadiyata baya nuna cewa jami'an DSS ne."

"Muna kara jaddada cewa babu wani dalili da zai sa hukumar ta musanta labarin tsare wani idan har ita ta tsaresu."

A Ranar 2 ga Watan Agusta, 2019, wasu Mutane da ba a san su wanene ba, su ka sace Abubakar Idris (Dadiyata) daga gidansa cikin tsakar dare Garin Kaduna.

Daga wannan lokaci zuwa yanzu, kusan watanni buyar, ba a sake jin labarin inda wannan Bawan Allah da ya yi fice wajen sukar gwamnatin APC ya shige ba.

Domin ganin an dawo da Mai gidanta, Mai dakin wannan Matashin Malamin jami’ar tarayya da ke Dutsinma, Khadija Ahmad, ta shigar da DSS kara a kotu.

Khadija Ahmad ta na bukatar jami’an DSS da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kaduna, da gwamnatin jihar su fito da Mai gidanta ba tare da wata-wata ba.l

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel