Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga jahar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya

Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga jahar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah Ya yi ma wakilin mazabar Garki/Babura ta jahar Jigawa a majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Adamu Fagengawo rasuwa a ranar Talata, 31 ga watan Disamba a kasar Dubai.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito wata majiya daga dangin mamacin ta tabbatar da mutuwarsa, inda tace dan majalisar ya yanke jiki ya fadi ne a gidansa, daga nan aka dauke shi a jirgin sama ba’a tsaya ko ina ba sai a asibitin Dubai.

KU KARANTA: Sai bango ya tsage: Kalli hotunan jami’in bankin daya shirya fashi da makami a bankin Abuja

Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga jahar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya
Adamu
Asali: Facebook

Sa dai kash! Ko kafin a isar da shi zuwa asibitin na ksar Dubai, tuni ya rigamu gidan gaskiya, domin kuwa a can ne likitoci suka tabbatar da da mutuwar tasa ga iyalansa.

Idan za’a tuna shi ma dan majalisar dokokin jahar Sakkwato na jam’iyyar APC dake wakiltar mazabar Kebbe a majalisar, Alhaji Isah Harisu ya rigamu gidan gaskiya a wani mutuwa da za’a iya bayyana shi a abin al’ajabi.

Dan majalisa Isah Harisu ya rasu ne da sanyin safiyar litinin, 30 ga watan Disamba inda ya yanke jiki ya fadi yayin da ake tsaka da zaman majalisar, daga nan shi kenan sai mutuwa. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!

Sai dai koda ya fadin, abokansa yan majalisa sun yi ta maza inda suka garzaya da shi zuwa babban asibitin koyar na jami’ar Usmanu Danfodiyo domin farfado da shi, amma a can ma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.

Isa Harisu, fitaccen dan siyasa ne a jahar Sakkwato da ya rike mukamai da dama a gwamnatin jahar, daga ciki har da mai baiwa gwamna shawara kafin ya shiga zauren majalisa, kuma ya taba zama dan takarar kujerar mataimakin Kakakin majalisar dokokin jahar Sakkwato.

Da fatan Allah Ya jikansu duka, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel