Badakalar daukan aiki: Matawalle ya dakatar da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara

Badakalar daukan aiki: Matawalle ya dakatar da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar da ake zargi da badakala a daukar ma'aikata.

Da yake magana a kan lamarin, kwamishinan kudi na jihar, Rabiu Garba, ya ce ma'aikatan da aka dakatar sun hada da darektan kudi na ma'aikatar kula da asibitocin jiha, darektan albashi na jihar da mataimakinsa da kuma sauran wasu ma'aikata biyar a ma'aikatar kudi ta jihar.

Ya ce ma'aikatan da aka dakatar sun jawo wa jihar Zamfara asarar miliyan N216 wajen biyan albashin ma'aikatan bogi.

Badakalar daukan aiki: Matawalle ya dakatar da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara; Bello Muhammed Matawalle
Asali: Facebook

Garba ya kara da cewa daya daga cikin wadanda aka dakatar din yana karbar albashin likitoci uku a kowanne wata.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar hana cakuda Maza da Maza a adaidaita

Kazalika, ya bayyana cewa za a agurfanar dasu da zarar an kammala gudanar da bincike a kansu.

"Wannan ita ce babbar matsalar da jihar Zamfara ta fuskata da har ta jawo gwamnati ta gaza fara biyan sabon karin albashi," a cewar Garba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel