Badakalar N6.3bn: Kana da kashi a gindi - Kotu ta bayyanawa Jonah Jang

Badakalar N6.3bn: Kana da kashi a gindi - Kotu ta bayyanawa Jonah Jang

A ranar Talata, Alkalin babbar kotun jihar Plateau, Mai shari'a Daniel Longji, ya bayyanawa tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, cewa yana da kashi a gindi kan zargin almundahanar N6.35bn da hukumar EFCC ke masa.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta shigar da Jonah Jang da tsohon kashiyan ofishin sakataren jihar, Yusuf Pam, kotu ne kan zargin yaudara da almundahanar kudin al'ummar jihar Plateau.

Bayan hukumar EFCC ta gabatar da shaidu 14, Jonah Jang ya bayyanawa kotu cewa babu laifin da ya aikata kuma ba shi da kashi a gindi.

Ya bukaci kotun tayi watsi da karar kuma ta wankesa a idon duniya cewa babu wani laifi da aikata.

DUBA NAN: Buratai ya karawa jami'an Soji 5 girma kan jaruntar da suka nuna wajen yakan Boko Haram

Amma yayinda aka dawo zama a yau Litinin a garin Jos, Alkalin ya bayyana cewa lallai akwai kashi a gindin Jonah Jang kuma ya zama wajibi ya kare kansa kan zarge-zargen da ake masa.

Daga karshe, Alkali mai shari'a, Daniel Longji, ya bayyana cewa zai ajiye shari'arsa domin a mikawa wani Alkalin saboda zai yi titaya bayan kwashe shekaru 45 a bakin aiki.

A wani labarin mai alaka, Babbar kotun tarayya dake zaune a jihar Legas ta kama tsohon gwamnan jihar Abiya kuma bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, da laifin almundahanar N7.2bn.

Kotun ta yanke masahukuncin shekaru 12 a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel