Rundunar soji ta bayyana dalilin da yasa motar yakinta ya babbake a Damaturu

Rundunar soji ta bayyana dalilin da yasa motar yakinta ya babbake a Damaturu

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Talata, 31 ga watan Nuwamba, ta ce matsalar na’urar lantarki ne ya haddasa fashewar motar yakinta a Damaturu, jihar Yobe a ranar Litinin.

Tarwatsewar motar da wutar da ke ta tashi ya haifar da tashin hankali a birnin. Sojoji uku sun ji raunuka da dama a yanayin.

Kyaftin Njoka Irabor, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sashi 2, na Operation Lafiya olee ya bayyana hakan a wani jawabi. jawabin ya zo kamar haka: "An samu tashin hankali a garin Damaturu sakamakon karar fashewar wasu abubuwa a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba. "Lamarin tashin wutan ya afku ne lokacin da wata motar yaki ke a hanyar komawa sansani aga wani aiki, sai wani waya ya samu matsala.

"Wannan ya yi sanadiyar babbakewar motar sannan ya kama da wuta.

"Lamarin ya afku ne a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri. "Motar ya babbake baki daya, yayinda dakarun da ke motar suka yi nasarar fitar da kansu a tashin wutar.

"Sai dai sojoji uku sun ji rauni sannan tuni aka kai su cibiyar lafiya domin samun kulawar likitoci.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya za ta janye dakarunta daga arewa maso gabas

"Sannan, Hedkwatar sashi na 2 na Operation Lafiya DDole, na fatan amfani da wannan damar don bukatar mazauna Damaturu da kewayensu a su tafi harkokin gabansu, domin dakarunmu za su cigaba da aiwatar da ayyukansu domin kare rayuka da dukiyoyi."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel