Rikicin APC: Gwamnoni 10 ke marawa Oshiomole baya

Rikicin APC: Gwamnoni 10 ke marawa Oshiomole baya

Tuggun kokarin tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na cigaba da bunkasa amma da alamun gwamnonin dake goyon bayansa sun fi yan adawarsa yawa.

Gwamnonin dake kira ga cire Oshiomole na ikirarin cewa shi ya sababbawa jam'iyyar asarar wasu jihohi a zaben 2019 da jam'iyyar PDP ta samu a banza.

Sun bayyana cewa muddin ana son sulhu tsakanin 'yayan jam'iyya musamman a jihohin Zamfara, Edo, Rivers, Ogun, da Imo, ya zama wajibi a fitittiki Oshiomole.

Hakazalika rikicin cikin gida da yake fama da shi a jiharsa ta Edo inda ya shiga takun tsaka da gwamnan jihar, Godwin Obaseki.

Amma masu goyon bayan Oshiomole sun bayyana cewa Oshiomole ya taimakawa jam'iyyar wajen samun nasara a zabukan jihar Osun, Ekiti, Bayelsa da Kogi kuma saboda haka a barshi ya cigaba da aikinsa.

DUBA NAN: Sau 27 Boko Haram da ISWAP suka kawo hari cikin kwanaki 14

Daga cikin gwamnonin dake bayan Oshiomole sune; Babjide Sanwo Olu (Lagos), Umaru Zulum (Borno), Dapo Abiodun (Ogun), Yahaya Bello (Kogi), Abdullahi Ganduje (Kano), Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe), Aminu Bello Masari (Katsina), Abdul Rahman Adbul Razaq (Kwara), Adegboyega Oyetola (Osun), da Simon Lalong (Plateau).

Gwamnonin dake kokarin cire Oshiomole sune Godwin Obaseki (Edo), Mallam el-Rufai (Kaduna), Kayode Fayemi (Ekiti), Rotimi Akeredolu (Ondo), Badaru Abubakar (Jigawa), and Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi).

Gwamnoni yan ba ruwanmu sune Abubakar Sani Bello (Niger), Abdulahi Sule Nasarawa, da Mai Mala Buni (Yobe).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel