Sau 27 Boko Haram da ISWAP suka kawo hari cikin kwanaki 14

Sau 27 Boko Haram da ISWAP suka kawo hari cikin kwanaki 14

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa sau 27 yan ta'addan Boko Haram da ISWAP suka kai hari yankin Arewa maso gabas cikin makonni biyu da suka gabata.

Babban hafsan mayakan ruwa, Ibok Ekwe-Ibas, ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawar da hafsoshin tsaro suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Litinin.

Ya ce jaruman Sojin sun dakile hare-haren kuma sun hallaka kwamandojin yan ta'addan da dama.

Babban jami'in tsaron ya kara da cewa dakarun Sojin Najeriya suna samun gagarumin nasara wajen yakan yan ta'addan.

A cewarsa, shugaban kasa ya basu umurnin tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas da sauran sassan Najeriya.

Baya ga haka, ya bayyana cewa a sabuwar shekarar 2020, da yiwuwan jami'an sojojin su janye daga yankunan da aka rikici domin baiwa yan sanda dama cigaba daga inda suka tsaya.

Manyan jami'an tsaron da suka halarci zaman sune shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Gabriel Olonosakin; babban hafsan mayakan sama, AM Abubakar Sadique; babban hafsan ilmin leken asiri, AVM Mohammed Usman; shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi.

Sauran sune mai bada shawara kan tsaro NSA, Babagana Munguno; Sifeto Janar na yan sanda, IG Mohammed Adamu; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da kuma wakilin babban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Lasisi Adeosun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel