Asiri ya tonu: An kama tireloli guda 2 makare da magunguna na bogi za'a shiga dasu jihar Kano

Asiri ya tonu: An kama tireloli guda 2 makare da magunguna na bogi za'a shiga dasu jihar Kano

- Hukumar haraji ta jihar Kano ta kwace wasu manyan motoci biyu dankare da magungunan bogi da lalatattu

- Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya jagoranci samamen da suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu

- Hakazalika, an tada kasuwar magani dake Sabon Gari zuwa Dangwauro dake karamar hukumar Kumbotso a jihar

Hukumar haraji ta jihar Kano ta kwace manyan motoci biyu dankare da magunguna na bogi tare da wadanda suka lalace a jihar.

Kamar yadda takardar da ta fito daga ma'aikatar lafiya ta jihar ta bayyana, ta kuma samu saka hannun jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, Isma'il Gwammaja da shugaban hukumar, kuma kwamishinan ma'aikatar lafiya ta jihar, Dr Aminu Tsanyawa.

Kwamishinan lafiyar ne yayi jagora wajen kama motocin bayan sun samu bayanan sirrin isowar motocin.

Takardar tace, an kama motocin ne a wani kangon gini a Unguwar Dabai dake karamar hukumar Dala ta jihar.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An cire dokar raba maza da mata a kasar Saudiyya

Takardar ta kara da bayyana cewa, gwamnatin jihar ta shirya don shawo kan matsalar siyarwa tare da shan miyagun kwayoyi ko kuma magungunan bogi "ballantana a tsakanin matasa da mata a jihar".

Takardar ta kara da cewa, gwamnati ta saka tsauraran matakai a kan ta'ammali da miyagun kwayoyi kuma ta umarci kasuwar magani ta Sabon Gari da ta koma Dangwauro a karamar hukumar Kumbotso dake jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel