Yadda wani mahaifi ya kashe yaransa 2 a jahar Ebonyi, 1 ya sha da kyar

Yadda wani mahaifi ya kashe yaransa 2 a jahar Ebonyi, 1 ya sha da kyar

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ebonyi ta sanar da kama wani Uba, Chinasa Ogbaga daya kashe yaransa guda biyu tare da ji ma daya mummunan rauni a kauyen Okpuitumo na karamar hukumar Abakalikin jahar Ebonyi.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin hira da ta yi da kamfanin dillancin labarun Najeriya a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Yan fashi sun bindige babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci, sun tasa keyar direbansa

A jawabinta, Yarsanda Loveth, ta ce Ogbaga ya tafi gidan tsohuwar matarsa ne inda ya kwashi yaran da nufin yin saye sayen bikin Kirismeti, yayin da suke kan hanya sai ya kauce ya shige cikin daji, inda ya yi amfani da adda wajen yi ma guda biyu daga cikinsu yankan rago.

“DPO na Yansandan Ekumenyi ne ya kai rahoton kisan kan zuwa shelkwatar Yansandan jaha, a yanzu haka dai mun kama wanda ake zargi da aikata laifin kashe yaran nasa guda biyu da kuma raunata daya mummunan rauni, wanda sana’ar facin tayan mota yake yi. Ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Disamba” Inji ta.

Daga karshe Loveth ta bayyana cewa a yanzu haka sun fara gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, kuma zasu gurfanar da shi gaban kotu da zarar sun kammala binciken. Haka zalika ta jaddada manufar rundunar Yansanda na tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

A wani labarin kuma, gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da hari a kan wani babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci na jahar Kogi, Bala Muhammed, inda suka bude masa wuta, sa’annan suka yi awon gaba da direbansa.

Wannan lamari ya faru ne a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja yayin da Alkalin ke kan hanyarsa ta halartar gasar kwallon Kwando a Ajanah, a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba da misalin karfe 4 na rana.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Alkalin da direbansa na gab da garin Itakpe ne a lokacin da yan fashin suka tare motar tasu, ba tare da bata lokaci ba suka harbe shi a hannu, sa’annan suka kwace duk wasu muhimman abubuwa da suka gani a motar, sa’annan suka tafi da direbansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel