Barazanar ISWAP: Gwamnoni sun bukaci Buhari ya dakatar da kudirin janye dakaru

Barazanar ISWAP: Gwamnoni sun bukaci Buhari ya dakatar da kudirin janye dakaru

Dakarun sojin Najeriya zasu janye daga wuraren tsaron cikin gida a sassan kasar nan a farkon shekarar 2020. An yanke wannan hukuncin ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron shuwagabannin tsaro a Abuja a ranar Litinin.

Jim kadan bayan wannan taron, wasu gwamnoni sun roki gwamnatin tarayya a kan kada ta janye dakarunta daga jihohinsu.

Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na jihar Benuwe, Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Hukuncin gwamnatin tarayyar na janye dakarunta ya biyo bayan sabbin barazanar mayakan ISWAP ne da a halin yanzu suka hada kai da mayakan Boko Haram.

A makon da ya gabata ne ISWAP ta watsa wani faifan bidiyonta a yanar gizo inda ta nuna yadda ta tsinke kawunan wasu mabiya addinin Kirista 10 a ranar Kirsimeti.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan Shi'a a Sokoto

Amma kuma, taron shugabannin tsaron sun bayyana cewa zasu gabatar da bincike mai tsanani a kan wuraren da ya kamata su janye dakarun.

Taron ya yanke shawarar cewa, jami’an ‘yan sanda ne ke alhakin samar da tsaron cikin gida a hannunsu don haka su zasu maye gurbin sojojin.

Shugaban ‘yan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, wanda ya zanta da manema labaran gidan gwamnati don bayyana makomar taron, ya bayyana cewa janye dakarun sojin zai basu damar mayar da hankali wajen tsaron kasar game da abubuwan da ka iya tasowa daga kasashen duniya.

Ekwe Ibas ya lissafo banga, garkuwa da mutane, tarwatsa bututun man fetur, a matsayin kalubalen cikin gida. Jami’an ‘yan sandan ne zasu tabbatar da shawo kan wadannan lamurran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel