Yan fashi sun bindige babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci, sun tasa keyar direbansa

Yan fashi sun bindige babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci, sun tasa keyar direbansa

Gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da hari a kan wani babban Alkalin kotun shari’ar Musulunci na jahar Kogi, Bala Muhammed, inda suka bude masa wuta, sa’annan suka yi awon gaba da direbansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja yayin da Alkalin ke kan hanyarsa ta halartar gasar kwallon Kwando a Ajanah, a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba da misalin karfe 4 na rana.

KU KARANTA: Ganduje zai kashe naira biliyan 2.5 don gina manyan asibitoci a sabbin masarautu

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Alkalin da direbansa na gab da garin Itakpe ne a lokacin da yan fashin suka tare motar tasu, ba tare da bata lokaci ba suka harbe shi a hannu, sa’annan suka kwace duk wasu muhimman abubuwa da suka gani a motar, sa’annan suka tafi da direbansa.

Jim kadan bayan aukuwar lamarin ne sai aka garzaya da Alkalin zuwa babban asibitin garin Okene, daga nan kuma aka mika shi zuwa garin Lokoja domin samun cikakkiyar kulawar da ta kamata.

A yan kwanakin nan an yi ta samu karuwar ayyukan yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makami a kan hanyar Lokoja zuwa Okene, ko a kwanakin baya sai da yan bindiga suka bude ma yan kwallon kungiyar Ifeanyi Ubah FC wuta a kan hanyar.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kauyuka guda hudu dake cikin karamar hukumar Dutsanman jahar Katsina, inda suka sace mutane uku tare da awon gaba da shanu da dama.

Yan bindigan sun yi awon gaba da mutane biyu a kauyen Maitsani da suka hada da Sale Rahama da Bilkisu Sunusi, sa’annan suka dauke Alhaji Bello Suke a kauyen Darawa. Yayin da a kauyen Madagu kuwa suka tattara shanu 60 da tumaki 40, haka zalika sun kwashe dabbobi da dama daga kauyen Gefen Kubewa, duk a cikin karamar hukumar Dutsanma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel