Sanata Abaribe ya bukaci Buhari ya saki El-Zakzaky

Sanata Abaribe ya bukaci Buhari ya saki El-Zakzaky

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, a ranar Talata ya yi kira ga fadar shugaban kasa ta karasa abinda ta fara ta sako Sheikh Ibrahmm El-Zakzaky da sauran wadanda ke halin da ya ke ciki kamar tsohon mai bayar da shawara kan tsaro, Sambo Dasuku da dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore.

Sanarwar da mai bashi shawara a kan fanin kafafen watsa labarai, Uchenna Awom ya fitar ta ce Abaribe ya yi wannan jawabin ne bayan sakin Dasuki da Sowore kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban na marasa rinjaye ya ce shima El-Zakzaky da sauran wadanda ake tsare da su duk kotu ta bayar da su beli.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Abaribe ya ce, "Ya kamata fadar shugaban kasa ta yi amfani da wannan damar da saki sauran; Bai dace a rika ganin kamar suna nuna banbanci ba. Kuma ya zama dole gwamnatin tarayya ta rika biyaya ga doka a dukkan lokuta.

"Bisa ga dukkan alamu sauran kasashen duniya za su mayar da kasar mu saniyar ware idan ta cigaba da watsi da umurnin kotu. Ya zama dole mu mutunta dukkan hukumomin gwamnati tare da girmama rabe-raben iko. Wannan shine yadda ake gudanar da mulki a demokradiyya."

Mabiya Zakzaky sun yi watsi da ikirarin da Ministan shari'a kuma Attoney Janar, Abubakar Malami ya yi na cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya sakin sa ba kan cewa gwamnatin jihar Kaduna ne ke tuhumarsa inda suka ce hukumomin gwamnatin tarayya ne ke tsare da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel