Abu kamar wasa: Budurwa ta kashe kanta da kanta bayan sahibinta ya ci amanarta

Abu kamar wasa: Budurwa ta kashe kanta da kanta bayan sahibinta ya ci amanarta

Wata budurwa mai suna Joy Osain dake zaune a unguwar Agbura cikin karamar hukumar Yenagoa na jahar Bayelsa ta kashe kanta bayan samu sabani da saurayinta, Eze Augustus dan shekara 28 saboda zarginsa da cin amanarta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lamarin ya auku ne a ranar washegarin Kirismeti, 26 ga wata Disamba, inda aka jiyo masoyan biyu suna cacar baki a tsakaninsu a gidan saurayin dake kauyen Azikoro dake cikin garin Yenagoa na jahar Byelsa.

KU KARANTA: Musulmai ba za su amince da dokar daidaita mata da mata a rabon gado ba - Sultan

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa: “Saurayin ta ya kaurace mata ne a ranar Kirismeti, don haka washegari sai ta tafi dakin sa, inda ta tarar da wata budurwa a ciki, daga nan ranta ya baci, suka dinga fada, amma ya doke ta.

“Bayan nan mun ji ta tana ta maimaita cewa ba za ta rayu a idon ta wata mace ta kwace mata saurayinta ba, bamu taba tsammanin da gaske take ba, daga nan kawai sai ji muka yi ta kwankadi fiya fiyan Sniper ta mutu.” Inji shi.

Sai dai a wani kaulin kuma, an bayyana cewa saurayin ne ya lakada mata dan banzan duka, sa’annan ya dura mata fiya fiya a cikin bakinta domin a yi zaton ita ta kashe kanta, bayan nan ne sai yan uwanta suka far ma gidan saurayin, inda suka yi kaca kaca da gidan.

Shi ma mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace tuni sun kama saurayin, sa’annan zasu kaddamar da binciken kwakwaf don gano gaskiyar lamarin.

A wani labarin kuma, mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana rashin amincewar al’ummar Musulmai da kudurin dokar daidaita maza da mata a kan abin da ya danganci rabon gado.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel