Musulmai ba za su amince da dokar daidaita maza da mata a rabon gado ba - Sultan

Musulmai ba za su amince da dokar daidaita maza da mata a rabon gado ba - Sultan

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana rashin amincewar al’ummar Musulmai da kudurin dokar daidaita maza da mata a kan abin da ya danganci rabon gado.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sultan ya bayyana kudurin dokar a matsayin abin da ya saba ma dokokin addinin Musulunci, don haka Musulman Najeriya ba zasu taba amincewa da ita ba.

KU KARANTA: Gasar Firimiya: Ba zan kashe kai na a kan Arsenal ba – Inji Atiku Abubakar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kudurin dokar ta tanadi kawo daidaito tsakanin mace da namiji wajen rabon gadon kudi ko kadara, haka zalika ta bukaci a baiwa mata yaranta bayan mutuwar mijinta sai dai idan yaran ba su son haka, ko kuma zai shafi walwalarsu.

Kudurin ta bukaci matar da mijinta ya mutu tana da daman auren duk wanda take so, kuma tana yancin samun gadonsa, bugu da kari tana da yancin cigaba da zama a gidan marigayin mijin nata.

“Addininmu ya tanadi tsarin rayuwa gaba daya, don haka ba zamu amince da duk wani tsarin haramta mana abin da Allah Ya umarcemu ba. Musulunci addini ne na zaman lafiya, mun dade muna zaman lafiya da kiristoci da sauran addinai daban daban a kasar nan, don haka a kyalemu mu yi addininmu yadda ya kamata.” Inji shi.

Daga karshe Sultan ya bayyana farin cikinsa da nasarar da gwamnatin tarayya, tare da dakarun Sojin Najeriya suke samu wajen yaki da kungiyar ta’addanci na Boko Haram, sa’annan ya yi kira ga shuwagabannin siyasa dasu kasance masu gaskiya da rikon amana.

A wani labarin kuma, tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon sakataren jam’iyyar CPC, Alhaji Buba Galadima ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.

Jaridar Blueprint ta ruwaito Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da gidan jaridar Daily Independent, inda yace idan har shugaba Buhari ya cika masa burinsa, ba zai bukaci kudi daga gwamnatin tarayya kafin ya shirya zabe ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel