Buhari ya bawa matasa shawara a kan aure

Buhari ya bawa matasa shawara a kan aure

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci matasan 'yan Najeriya a kan yadda zasu gina kyakyawar rayuwar aure mai inganci.

A ranar Juma'a ne 27 ga watan Disamba shugaban kasar yayi wannan kiran ga matsan Najeriya. Ya bukace su da su nemi sanin magabata kuma kwararru a ilimin zamantakewa kafin yin aure.

Yace neman sani daga wajen wadanda suka gogu a harkar kuma masu halayya ta gari, zai tabbatar da cewa auren ya dade tare da wuce duk wani tsiradi da zai iya fuskanta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan ne a birnin Kano yayin da yake taya dan shugaban majalisar dattijan Najeriya Ahmad Lawan, murnar auren da yayi a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: A yayin da ake rade- radin mutuwarsa, IBB ya bayyana shirinsa na yin aure bayan shekara 10 a matsayin gwauro

Wannan sakon daga shugaban kasa, ya isa wajen daurin auren ne ta hannun wakilansa da ya tura. Sun hada da ministan birnin tarayyya, Mohammed Musa Bello, ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai murabus, ministan aikin noma, Alhaji Sabo Nanono da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.

A sakon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce: "Idan kana bukatar wata shawara a kowanne fanni na rayuwa, toh ba shakka ka nemi wadanda suka zamo misali nagari a wannan bangaren.

"Babban misali shine Sanata Lawan. A siyasa da rayuwa gaba daya ya kasance ya mallaki kyawawa kuma nagartattun halaye."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel