Ban san iya sau nawa na kwanta da maza a rayuwata ba - Budurwa

Ban san iya sau nawa na kwanta da maza a rayuwata ba - Budurwa

- Queen Farcadi sananniya ce a kafofin sada zumuntar zamani a kasar Ghana

- Ta bayyana cewa rashin samun aiki ne yasa ta fara kwanciya da maza bayan da ta gano ta mallaki abinda suke so

- Ta ce, ta zubar da ciki sau da yawa tun tana da karancin shekaru a duniya

Queen Farcadi sananniya ce a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram. Sananniyar 'yar kasar Ghana din ta ce ta kwanta da mazan da ba zasu kirgu ba.

A yayin da ta bayyana a wani shirin gidan talabijin mai suna Delay Show, wanda ake yi kai tsaye, Queen tayi magana a kan rayuwar jima'inta da kuma dalilin da yasa ta kwanta da maza masu tarin yawa.

Queen ta ce ta fara kwanciya da maza ne sakamakon rashin samun aiki bayan da ta nema a wurare masu tarin yawa na tsawon lokaci. Tace daga nan ne ta yanke shawarar fara amfani da jikinta bayan da ta gane zata kasance haja mai kyau a kasuwar saboda tana da abinda maza ke so.

KU KARANTA: Tashin hankali: Dan Acaba yayi hadari ya mutu ya bar mata 6 da 'ya'ya 30

Ta fara wallafa hotunan tsiraici a kafafen sada zumuntar zamani ballantana Instagram. Daga nan ne masu sonta da kuma mabiyanta suka karu kuma maza suka fara kawo kansu.

Ta kara da bayyana cewa, ba zata iya kirga mazan da ta kwanta dasu ba.

Queen Farcadi ta tabbatar da cewa ta zubar da ciki sau da yawa tun tana da karancin shekaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel