Hotunan daurin auren dan shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
A ranar Juma'a 27 ga watan Disamban 2019 ne Ibrahim Lawan, babban dan shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya auri amaryarsa Amani, da aka ce diyar hamshakin dan kasuwa na Kano, Alhaji Bala Umar ne.
An fara bukukuwan auren ne a ranar Laraba 25 ga watan Disamba inda aka yi kamun amarya, sannan aka yi taron cin abinci a ranar Alhamis 26 ga watan Disamba.
An daura auren ne a ranar Juma'a 27 ga watan Disamba a masallacin Al Furqan a Kano inda babban limamin masallacin Dakta Bashir Aliyu Omar Sadaki ya daura auren.
Ministan sadarwa Dakta Isa Ali Pantami ne waliyin Amani yayin da gwamnan jihar Yobe, Mai Bala Buni kuma shine ya karbi auren a madadin angon.
DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)
Wasu daga cikin manyan bakin da suka hallarci daurin auren sun hada da Jagora a majalisa, Dakta Yahaya Abdullahi, Kakakin Majalisar Wakilai na tarayya, Hon. Femi Gbajabiamila, Sanata Uba Sani, shugaban hafsin sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar da tsaffi gwamnoni da ministoci har ma da wadanda ke kan mulki a yanzu.
Ga dai hotunan a kasa:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng