Yadda wata mata ta makance bayan yaranta sojoji 2 sun mutu wurin yaki da Boko Haram

Yadda wata mata ta makance bayan yaranta sojoji 2 sun mutu wurin yaki da Boko Haram

Rasuwar 'ya'yan wata mata sakamakon yaki da Boko Haram ya sa ta shiga halin rashi da ya yi sanadin makancewarta.

Malama Aisha Umar da aka fi kira da Indo wacce tana daya daga cikin iyayen da 'ya'yansu suka rasu yayin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Matar mai shekaru 45 tana zaune ne da iyayen ta a Unguwar Dandinshe a karamar hukumar Dala na jihar Kano inda ta ke neman taimakon yadda za ta yi ta yi maganin matsalar idon ta.

Kafin yanzu, tana zaune ne a barikin soja na Jaji da ke Kaduna tare da 'ya'yan ta biyu da suka tashi da sha'awar shiga aikin soja kuma daga bisani suka zama sojojin.

A hirar da ta yi da Daily Trust, ta ce "Saboda sha'awar aikin soja, 'ya'ya na Mubarak da Abubakar Hassan sun shiga aikin soja. Mubarak na aiki da Kaduna yayin da Abubakar kuma yana Abia. Bayan wani lokaci an tura Mubarak zuwa Maiduguri inda ya yi shekaru biyu kafin ya kamu da rashin lafiya.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

"Ba mu sani ba sai bayan da rashin lafiyar ya yi tsanani. Kwamandan su ya kira ni mu tafi mu duba shi amma kafin mu tafi sai aka kira mu aka ce ya mutu."

Ta ce mutuwar ya yi mata ciwo sosai amma dayan dan ta Abubakar ya zama mata abin kwantar da hankali. "Abubakar yana fada min cewa dole ko wane rai sai ya dandani mutuwa. Ya ce sau biyar sunansa na fitowa amma ba a tura shi Borno ba."

Sai dai daga karshe an tura shi Maidugurin. Mahaifiyar ta ce ta masa addu'a kafin ya tafi.

Bayan watanni hudu, ya dawo ya ziyarci mahaifiyarsa amma ya sake komawa filin daga. Bayan kimanin watanni uku, Abubakar da wasu sojojin sun mutu sakamakon fashewar bam a Sabon Garin Damboa inji mahaifiyar.

Ta ce an ba ta N500,000 domin jana'izarsu amma bayan hakan ba ta sake samun wani kudi ba yayin da mahaifinsu ke kokarin karbar allawus dinsu. Ta ce mahaifin ya tuntubi wasu sojoji da ke taimaka masa domin kudin su fito amma har yanzu ba su cimma nasara ba.

Mahaifiyar sojojin kuma tana fama da ciwon ido inda ta ce ta ziyarci wani asibitin kudi a Kaduna kuma likitoci suka tabbatar cewa hawan jini ne ya janyo makancin a idonta daya. Dayan idon ya fara ciwo kuma ta tafi Asibitin ido na kaduna inda ta fara karbar magani sai dai da kyar da ke iya biyan kudin maganin duba da cewa 'ya'yan ta ne kai taimakawa kuma yanzu sun mutu.

Aisha tana kira ga mahukunta da sauran al'umma su tallafa mata domin mijinta ba shi da karfi kuma ta gano wani asibiti da za a yi mata aiki a idanun biyu don ta fara gani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel