Kaico: Yadda Boko Haram suka kashe amarya da kawayenta a hanyarsu ta zuwa daurin aure

Kaico: Yadda Boko Haram suka kashe amarya da kawayenta a hanyarsu ta zuwa daurin aure

- 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kashe wata amarya da kawayenta

- 'Yan ta'addan sun halaka amaryar, Martha Bulus ne a garin Gwoza a hanyarsu ta zuwa Jimeta a jihar Adamawa

- An shirya daura auren Martha Bulus ne da angonta Mista Joseph Amos Zamdai a ranar 31 ga watan Disamban 2019

Mayakan kungiyar ta'ada na Boko Haram a garin Gwoza sun kashe wata amarya mai suna Martha Bulus tare da kawayenta a hanyarsu ta zuwa Jimeta, Yola a jihar Adamawa domin shirin daurin aurensu da aka shirya yi a ranar 31 ga watan Disamban 2019.

Garin Gwoza da ke hanyar zuwa Bama yana daya daga cikin garuruwan da 'yan ta'addan na Boko Haram suka dade suna kai hare-hare.

Wata mai amfani da shafin Twitter, Adetutu Balogun @Tutsy22 da ya wallafa labarin a ranar Juma'a ya ce an kashe amaryar da kawayenta a hanyarsu ta zuwa Adamawa.

Ta rubuta, "An kashe ta a hanyar ta na zuwa Gwoza a jiya domin daurin aurenta. An kashe ta tare da kawayenta."

Za a daura mata aure ne da angonta Mista Joseph Amos Zamdai.

DUBA WANNAN: An hango giwaye 250 a filin yakin Boko Haram a Borno (Hotuna)

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku labarin wata dattijuwa mai suna Malama Aisha Umar da aka fi kira da Indo wacce ta makance bayan 'ya'yanta sojoji biyu sun mutu yayin artabu da 'yan ta'addan Boko Haram.

Dattijuwa mai shekaru 45 tana zaune ne da iyayen ta a Unguwar Dandinshe a karamar hukumar Dala na jihar Kano inda ta ke neman taimakon yadda za ta yi ta yi maganin matsalar idon ta.

Kafin yanzu, tana zaune ne a barikin soja na Jaji da ke Kaduna tare da 'ya'yan ta biyu da suka tashi da sha'awar shiga aikin soja kuma daga bisani suka zama sojojin.

A hirar da ta yi da Daily Trust, ta ce "Saboda sha'awar aikin soja, 'ya'ya na Mubarak da Abubakar Hassan sun shiga aikin soja. Mubarak na aiki da Kaduna yayin da Abubakar kuma yana Abia. Bayan wani lokaci an tura Mubarak zuwa Maiduguri inda ya yi shekaru biyu kafin ya kamu da rashin lafiya.

"Ba mu sani ba sai bayan da rashin lafiyar ya yi tsanani. Kwamandan su ya kira ni mu tafi mu duba shi amma kafin mu tafi sai aka kira mu aka ce ya mutu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel