Hanya daya da namiji zai samu tsawon rayuwa ita ce ya nesanci mace - Tsohon shugaban kasar Kenya

Hanya daya da namiji zai samu tsawon rayuwa ita ce ya nesanci mace - Tsohon shugaban kasar Kenya

- Tsohon shugaban kasar Kenya, Daniel Arap Moi ya bayyana dalilin tsawon rai da yayi

- Yace gujewa mata da duk abinda ya dangancesu ne ke kawo tsawon rai tare da kwanciyar hankali

- Moi gogaggen dan siyasa ne wanda a zamanin mulkinshi ya juya akalar siyasar kasar Kenya

Tsohon shugaban kasar Kenya, Daniel Arap Moi ya bayyana sirrin doguwar rayuwa mai cike da annashuwa. Ya ce ana yin doguwar rayuwa ne idan aka gujewa mata ta kowanne bangare.

Tsohon shugaban kasar ya yadda cewa babban dalilin da yasa yayi dogon kwana shine saboda ya gujewa mata kuma yana mayar da hankali wajen sha'aninshi a barandar gidanshi dake Kabarak.

An haifa Moi ne a shekaru kadan bayan yakin duniya na farko. Da aka tambayeshi sirrin tsawon rai da farin ciki, sai Moi ya ce, "Sau da yawa ina zama a barandah ina shan iska tare da karnika na. Na tsani hayaniya shiyasa nake zama ni kadai."

KU KARANTA: Babbar magana: Na yaudari samari da dama, amma nima kuma an yaudare ni - Rayya

Daniel Arap Moi ya yi shugabancin kasar Kenya a 1978. A shekarun da ya kwasa a matsayin shugaban kasa, Moi da jam'iyyarshi ne ke juya akalar siyasar kasar da shari'a.

Moi kwararre ne kuma ya kasance haziki wajen shawo kan matsalolin kabilanci.

Kamar yadda wata jarida a kasar ta ce: "Koda Moi bai karanci siyasa a wata jami'a ba, ya tabbatar da cewa shi 'Farfesan siyasa' ne a aikace."

A shekarar 1982 ne Moi ya bi ta hannun 'yan majalisa ya mayar da kasar Kenya kasa mai jam'iyya daya. Duk da Kenya ta kasance kasa mai jam'iyya daya tun a 1969 lokacin da aka kori 'yan adawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel