Gargadi: An gano yadda wuraren sayar da abinci ke sanya Paracetamol a cikin nama domin ya dahu da wuri

Gargadi: An gano yadda wuraren sayar da abinci ke sanya Paracetamol a cikin nama domin ya dahu da wuri

- A gidaje da yawa da kuma wuraren cin abinci jama'a na cin guba da kansu ba tare da sun sani ba

- Dafa ganda da nama da akeyi da fanado shine aka gano ya zamo silar yawaitar ciwukan koda da hanta ga matasa

- Mata na amfani da fanado ne don adana gas, kalanzir da itacensu wajen dafa nama mai tauri

A gidaje da yawa da kuma wuraren cin abinci, ana amfani da kwayar fanado ne don dafa nama da gaggawa. Ana amfani da fanado na naira hamsin kacal don tseratar da gas, kalanzir ko kuma itace wajen dafa nama mai tarin yawa cikin mintoci kalilan. Lamarin da ban mamaki amma da dadi a wajen mata. Matsalar ita ce, muna gaggauta girkin ne amma muna gaggauta rage kwanakinmu a duniya.

"Gaskiya yafi sauki da sauri a dafa nama da fanado," in ji Adeola.

"Ina amfani da fanado wajen dafa ganda da kai da kafan sa a kowanne lokaci. Idan ka saka kwaya daya na fanado, naman ya kan narke tare da dahuwa cikin mintuna 10 kacal." Ta ce.

Amma Adeola na barazana ne ga rayuwarta da ta 'ya'yan kanana. Bata san hakan ba har sai da aka yi mata bayani dalla-dalla.

Asalin fanado amfaninshi kashe radadi ne idan aka sha shi. Yana maganin ciwon kai ko wani radadi dake damun dan Adam. Amma matukar aka dafa shi a tukunya, yana tafiya kai tsaye zuwa koda da hanta don lalatasu.

Masana sun sanar da cewa, idan aka dafa fanado, a kan cire sinadarin maganin dake tare dashi kuma ya koma abu mai matukar hatsari ga jikin dan Adam.

KU KARANTA: Ikon Allah: Wata mata ta haihuwa bayan shafe shekaru 13 dauke da ciki

Idan aka fara dafa fanado, ya kan koma 4-aminophenol, wanda masana suka ce yana da matukar hatsari ga hanta da koda.

A makon da ya gabata ne, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar Facebook ya bayyana yawaitar amfani da fanado da akeyi wajen dafa naman akuya wanda ake kira da farfesu a Uyo, jihar Akwa Ibom da kewaye.

Bincike daga marubucin ya bayyana yadda masu gidajen abinci ke amfani da fanado don yana rage musu kudin kalanzir da itace.

A cikin kwanakin nan, yawan matasa a Najeriya dake fama da ciwon koda ya yawaita. Sau da yawa lamarin na kaiwa ga mutuwa. Wannan binciken kuwa shine ya bayyanawa masana kiwon lafiya abinda ya dade da shige musu duhu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel