Ikon Allah: Wata mata ta haihu bayan shafe shekaru 13 dauke da ciki

Ikon Allah: Wata mata ta haihu bayan shafe shekaru 13 dauke da ciki

- Dorcas mata ce mai shekaru 58 a duniya wacce ta haifa yaro namiji a cikin watan Disamba

- Ta bayyana yadda ta cire rai da haihuwa saboda tun 2006 ta dena jinin al'ada

- Sun nemi taimakon likitoci da masu maganin gargajiya a cikin shekaru 35 da aurensu, amma sai yanzu aka samu rabon

Wata mata mai shekaru 58 a duniya mai suna Dorcas Osiebo, wacce ta dena jinin al'ada tun 2006 ba tare da alamar ciki ba, ta haifi yaro namiji.

Dorcas wacce ta haifi yaro namiji a ranar 13 ga watan Disamba ta sanar da Kamfanin dillancin labarai a ranar Laraba a Abuja cewa, ta dimauce kuma ta fada farin ciki a lokacin da matar fasto wacce ma'aikaciyar jinya ce ta tabbatar mata tana da ciki.

"Ma'aikaciyar jinyar ta dubeni ta ce, 'Mama, muna godiya ga Allah saboda kina da juna biyu.' Na sha mamaki".

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa Dorcas tayi aure da Christopher Osiebo mai shekaru 64 kuma ta cire ran haihuwa tunda sun shekara 35 ba haihuwa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kungiya ta nemi gwamnatin tarayya ta kyale karuwai su fara rijista a Najeriya

"Amma a farkon shekarar nan, naji a jikina ina da ciki. Amma sai nayi tunanin ba hakan bane saboda tun 2006 rabon da in ga al'adata," ta ce.

"Munyi aure tun a watan Janairu 1984 amma bamu samu haihuwa ba. Mutanen da duk muka yi aure tare sun haihu da 'ya'ya har da jikoki. Hatta kanwata na da jikoki," cewar Dorcas.

Ta ce sun nemi taimako daga wajen masu magugunan gargajiya da asibitoci amma ba biyan bukata.

Kamar yadda ta ce, ta daina jinin al'ada ne tun a 2006, kuma kanwarta da ta riga aure na da jikoki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel