Boko Haram ta kashe kiristoci 11 da ta kama a Borno a ranar bikin Kirismeti

Boko Haram ta kashe kiristoci 11 da ta kama a Borno a ranar bikin Kirismeti

Kungiyar ISWAP wanda aka fi sani da suna Boko Haram ta yi ma wasu kiristoci 11 kisan gilla a matsayin ramuwar gayyan kashe kwamandanta da mai magana da yawunta da Sojoji suka yi a cikin watan Oktoba.

BBC Hausa ta ruwaito Boko Haram ta bayyana kisan mutanen 11 ne cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafukanta na yanar gizo da suka hada da Amaq da Hoop, inda tace hukuncin kisan ya zo daidai ne da bikin kirismeti.

KU KARANTA: Zargin karkatar da kudin makamai: Kungiyar Izala ta ziyarci Sambo Dasuki don jajanta masa

A cikin bidiyon mai tsawon dakika 56, kungiyar ta bayyana cewa ta kama mutanne ne a jahar Borno a cikin makonnin da suka gabata, kamar yadda wani mai gabatar da jawabi ya bayyana jim kadan kafin halakasu.

Bidiyon ya nuna mutane 11 da aka daure fuskokinsu durkushe a kan gwiwowinsu a kasa sanye da wasu kaya masu launin ruwan goro, sa’annan kuma akwai wasu mayakan Boko Haram 11 da suke tsaye a kan kowannensu.

A jawabin mai gabatarwar cikin harshen Hausa, yace: “Wadannan da ku ke gani a gabanmu kiristoci ne da zamu zubar da jininsu domin ramuwar gayyar rayukan malamai masu daraja, Sarkin Musulmi Abu Bakr al-Baghdadi da kuma kaakakin daular Musulunci Abu al-Hasan al-Muhajir.”

Kammala jawabinsa ke da wuya, sai guda daga cikin yan ta’addan ya dirka ma wani daga cikin kamammun dake gabansa, sa’annan sauran yan ta’addan suka kwantar da wadanda ke gabansu suka datse wuyoyinsu.

A wani labarin kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.

Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudin makamai dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel