Mutane 2 sun mutu a harin da yan bindiga suka kai garuruwan jahar Kebbi

Mutane 2 sun mutu a harin da yan bindiga suka kai garuruwan jahar Kebbi

Akalla mutane biyu ne suka gamu da ajalinsu yayin da wasu gungun yan bindiga da ake tunanin barayin shanu ne suka kaddamar da samame a wasu kauyuka guda 9 na karamar hukumar Wasagu na jahar Kebbi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito yan bindigan sun kai samamen ne a kauyukan dake kan iyakar jahar Kebbi da Zamfara da misalin karfe 7 na dare a ranar Talata, 24 ga watan Disamba, inda suke bude ma jama’an wuta, sa’annan suka kwashe dabbobi da kudi.

KU KARANTA: Kodai ku tuba ku mika wuya, ko kuma karshenku ya zo kenan – Buhari ga miyagun Najeriya

Wani mazaunin yankin, Usman Mohammed ya bayyana kauyukan da hare haren ya shafa sun hada da Shengel, Duru, Wadako, Kawo, Auda, Dadin kowa, Mashigi, Zaggai da kuma Yar Kuka.

Usman ya bayyana cewa mazauna kauyen sun tsere zuwa kauyen Waje da Chonoko saboda gudun fadawa hannun yan bindigan, harin da aka kwashe tsawon kwanaki biyu ana kaiwa.

Shi ma kaakakin kwamishinan Yansandan jahar, DSP Nafiu Abubakar ya bayyana cewa yan bindigan sun shigo ne daga jahar Zamfara, kuma sun sace shanu da dama, sa’annan suka bindige mutane biyu, daga nan kuma suka tsere cikin daji kafin jami’an tsaro su bayyana.

Kaakakin yace yan bindigan sun kai harin cikin sauki ne sakamakon yanayin kauyen, amma yace a yanzu sun kara tsaurara matakan tsaro a yankin kauyukan domin kare sake aukuwar wani sabon hari.

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da samun nasarar cafke wasu kasurguman barayin shanu tare da kama dimbin makamai, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar, Habu Ahmed Sani ya tabbatar.

Kwamishinan Yansandan ya bayyana cewa barayin sun addabi yankunan jahohin Kaduna, Katsina da kuma jahar Kano, inda suke bi ruga rugan dabbobi suna kwashe shanun mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel