Da sauran rina a kaba: DSS ta kwace wayoyin salular Sowore bayan ta sake shi
Jami’an hukumar tsaron sirri, DSS, ta sako tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma fitaccen dan jaridar nan mai mallakin kamfanin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, sai dai ta hana shi wayoyin salularsa.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito a ranar Talata, 24 ga watan Disamba ne hukumar ta saki Sowore bayan umarnin da babban lauyan gwamnatin Najeriya, kuma ministan sharia, Abubakar Malami ya bayar.
KU KARANTA: Na daina zuwa makarantar Islamiyya ne saboda bulalar Malam – Obasanjo
Sai dai duk da cika wannan umarni na ministan sharia, hukumar DSS ta cigaba da rike wayoyin salular Sowore, wanda hakan ke nuna suna kokarin sa idanu ne a kan sadarwarsa da kuma mu’amalarsa da mutane. Amma har yanzu hukumar bata da wani kwakkwaran dalilin yin hakan ba.
A ranar 3 ga watan Agustan 2019 ne hukumar DSS ta kama Sowore dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar AAC, inda ya samu kuri’u 30,000 kacal. Sai dai hukumar ta sake shi a ranar 5 ga watan Disamba, amma daga bisani ta sake kamashi a ranar 6 ga watan Disamba.
A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sakin tsohon babban mashawarcin tsaro ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Kanal Sambdo Dasuki mai ritaya.
Ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Talata, 24 ga watan Disamba, inda yace gwamnati ta yanke shawarar sakin Sambo Dasuki da Sowore ne biyo bayan umarnin wasu kotuna ta hanyar bada belinsu.
“Muna kira ga mutanen biyu da su tabbata sun cika sharuddan belin da kotu ta gindaya musu, sa’annan su tabbata sun kauce ma aikata duk wani abu da ka iya tayar da hankula a kasa ko kuma barazana ga tsaron kasa.
“Haka zalika su kauce ma aikata duk wani abu da ka iya gurgunta shari’arsu dake gudana, wanda a za’a cigaba da ba tare da fashi ba kamar yadda dokokin kasa suka tanada.” Inji Malami.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng