Ma'aikatan Zamfara 4,972 ba za su samu albashin Disamba ba

Ma'aikatan Zamfara 4,972 ba za su samu albashin Disamba ba

A kalla ma’aikatan jihar Zamfara 4,972 ne zasu rasa albashin watan Disamba har sai an tabbatar da sahihancin kasancewarsu ma’aikatan jihar. Kwamishinan kudin jihar, Alhaji Rabiu Garba Gusau ya bayyana.

A yayin zantawa da manema labarai a Gusau, Rabiu ya ce tsarin albashin jihar na da wasu abubuwan dake ba a bayyane ba. A don haka ne akwai bukatar warwarewar matsalar.

Wannan ya bayyana ne bayan kwamishinan da babban sakatarensa sun jajirce wajen duba kididdigar kudin ma’aikatar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Ya ce kudin ma’aikatan da abun ya shafa sun kai naira miliyan 216. Ya kata da cewa, akwai wasu ma’aikatan da babu bayaninsu a ma’adanar bayanai ta CBN. Akwai wadanda sunansu kuwa bai daidaita da irin wanda aka samu a bankunansu ba.

DUBA WANNAN: Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

Sauran rashin daidaituwar sun hada da fiye da albashi daya a asusun banki daya, bayanin asusun banki ba tare da BVN ba, saka sunayen wadansu mutane da ba a tantance ba a matsayin ma’aikatan gwamnatin ba, ko kuma ba tare da amincewar gwamnan ba, shigar albashi wasu asusun bankuna bayan sun yi murabus da sauransu.

Kwamishinan kudin jihar ya bayyana cewa, duk wani ma’aikaci da ke da koke ya gabato don tantancewa. Ya kara da tabbatar da cewa, duk wanda aka kama da laifi wajen tantancewar za a cafkesa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel