El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

Babban sakataren majalisar Ahl-ul-Bayt ta duniya ya bayyana cewa dole ne kungiyoyi a duniya su assasa tambayoyi ga gwamnatin Najeriya, don duba lafiyar Zakzaky da kuma nemar masa lafiya.

Ramezani ya bayyana wannan ne a wata tattaunawar da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Iran. Anyi wannan tattaunawar ne da manema labarai a ranar tunawa da tashin hankalin da ya auku a Zaria karo na hudu tare da tunawa da garkame shugaban kungiyar IMN din, Ibraheem El-Zakzaky.

Babban sakataren majalisar Ahl-ul-Bayt ta duniya ya ce: "Kasashen musulunci ya kamata su bibiyi lafiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky tare da bukatar gwamnatin Najeriya ta yi bayani a kan hakan."

DUBA WANNAN: Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

"Halin da wannan babban mutumin ke ciki abun bibiya ne. Kuma kamata ya yi kungiyoyin duniya su yi hakan.. Wannan ba matsalar tsaro ba ce," ya jaddada.

"Dole ne kungiyoyin duniyar su bukaci gwamnatin Najeriya da ta mayar da hankali wajen duba lafiyar Zakzaky kuma a mika shi asibiti, ganin cewa likitoci da masana kiwon lafiya sun ja kunnen kasar a kan halin rashin lafiyar da yake ciki. Idonsa na hagu na makancewa kuma akwai yuwuwar shigar wasu cutuka ta nan," in ji Ramezani.

"Nuna halin ko-in-kula ga lafiyar Zakzaky da kungiyoyin duniya suka yi zai iya kawo manyan kalubale da ba za a iya shawo kansu ba a nan gaba," Ramezani ya ja kunne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel