Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma yayar Gwamna Yahaya Bello rasuwa

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma yayar Gwamna Yahaya Bello rasuwa

Gwamnan jahar Kogi Alhaji Yahaya Bello ya yi rashin babbar yayarsa, Hajiya Rabi’at Bello wanda Allah Ya yi ma rasuwa a ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, kamar yadda gwamnan da kansa ya bayyana.

Gwamna Bello ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook a ranar Talata, 24 ga watan Disamba, inda yace Hajia Rabi’at ta rasu tana da shekaru 59, ta rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma yayar Gwamna Yahaya Bello rasuwa

Hjaiya Rabiat
Source: Facebook

Legit.ng ta ruwaito Gwamna Bello yana bayyana rasuwar Hajiya Rabi’at a matsayin babban rashi ga kafatanin yan uwanta da abokan arzikinta, musamman ma iyalan gidan Alhaji Bello Ipemida Ochi.

Daga karshe gwamnan ya bayyana za’a yi sadakan uku na mamaciyar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba a gidanta dake unguwar Agassa, cikin garin karamar hukumar Okene na jahar Kogi.

A wani labari kuma, tsohon kwamishinan ayyuka a jahar Jigawa, hamshakin dan siyasa, fitaccen attajiri kuma babban basarake, Sarkin Yakin Kazaure, Injiniya Baba Aliyu Santali ya rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba.

Shugaban hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen jahar Kano, Zubairu Mato ne ya tabbatar da haka, inda yace hadarin ya rutsa da Baba Santali ne a kan hanyar Kano zuwa Kaduna a daidai Chiromawa Gadar Kifi cikin karamar hukumar Garun Malam.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mato ya bayyana cewa wani sundukin kaya da wata babbar mota ta dauko ne ya fado a kan motar Baba Santali, kuma ya dannesu, nan take suka mutu tare da direbansa.

Haka zalika, wani mummunan hatsari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 sakamakon wani mummunan hadari daya auku a kan babbar hanyar Funtua zuwa Zaria, a jahar Katsina, inda mutane da dama suka samu munanan rauni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel