Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan ta'adda a Biu

Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan ta'adda a Biu

Mazauna karamar hukumar Biu, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa wasu yan ta'adda sun kawo farmaki kuma Sojoji na kokarin dakilesu a yanzu haka.

Shahrarren dan jaridan da ya shahara da kawo labaran Boko Haram, Ahmed Salkida, ya tabbatar da hakan inda ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Ana musayan wuta a mahaifata Biu, jihar Borno. Hankulan al;ummar garin ya tashi kuma sun fara guduwa (daga muhallansu)."

"Ina fatan mahaifina mai shekaru 85 da sauran jama'a na nan lafiya kafin a kawo dauki."

"Hakazalika ba'a san wani bangaren yan ta'addan Boko Haram suka kawo harin ba."

Za ku tuna cewa kungiyar Boko Haram ta balle gida biyu; bangaren Abubakar Shekau da kuma bangaren Abu Mus'ab Al-Barnamwi masu suna ISWAP.

A jiya, Wasu Faifan bidiyoyi biyu sun bayyana a kafafan ra'ayi da sada zumunta kan yadda Sojojin Najeriya ke musayar wuta da yan tada kayar bayan Boko Haram

Rahotannin sun gabata kan yadda yan ta'addan sukayi kokarin kai farmaki Damaturu, babbar birnin jihar Yobe amma Sojojin suka dakilesu bayan kwashe sa'o'i ana artabu.

Majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa wannan da yammacin Lahadi ne yan sanda suka kai harin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel