Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

Akwai a kalla kusan manyan limaman addinin Kirista 10 da suka mallaki jiragen sama na kashin kansu.

Fasto David Oyedepo babban malamin Kirista ne dake shugabantar rukunin majami'un 'Livin Faith' na fadin duniya da 'Tabernacle megachurch' da kuma 'Faith Tabernacle'; wadanda manyan majami'u ne dake da mabiya a kalla 50,000 a nahiyar Afrika.

Oyedepo, haifaffen jihar Kwara, yana daya daga cikin manyan limaman addinin Kirista da suka mallaki jiragen sama na kashin kansu.

Akwai masu ganin cewa Bishop Oyedepo ya zarta sauran tsarorinsa; manyan limaman addinin kirista dake Najeriya, idan har maganar kudi ake yi. An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $100 zuwa $200 bayan manyan gidajen alfarma da motoci da yake da su, ga kuma zunzurutun kudi a cikin asusun bankuna.

DUBA WANNAN: Aljannar duniya: Hotunan cikin katafaren gidan Dangote da kudin da aka kashe

Sai dai, 'yan Najeriya da dama na sukar Limaman Kirista na Najeriya saboda gasar da suke yi da juna wajen sayen jiragen sama daga irin kudin da suke samu daga mabiyansu, wadanda mafi akasari talakawa ne.

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

A cikin jirgin sama Fasto Oyedepo
Source: UGC

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

Fasto Oyedepo a cikin jirginsa
Source: UGC

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

Fasto Oyedepo yana sauko wa daga jirginsa
Source: UGC

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3

Hotunan cikin jirgin sama da Faston Najeriya ya siya a kan biliyan N12.3
Source: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel