DSS ta gurfanar da Fasto kan zargin sace yaro a cocinsa

DSS ta gurfanar da Fasto kan zargin sace yaro a cocinsa

Hukumar DSS ta gurfanar da shugaban cocin Sotitobire Miracle Centre, dake Akure, jihar Ondo, Babatunde Alfa, a kotun majistare tare da wasu mambobinsa shida kan zargin sace wani yaro a cocinsa.

Alkalin kotun, Mrs Charity Adeyanju, ta bada umurnin garkamesu a gidan gyara halin Olokuta a jihar.

An sace yaro mai suna, Gold Kolawole, ne a ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba, 2019 a cocin da iyayensa ke zuwa ibada.

Mambobin da aka gurfanar tare da faston sune Omodara Olayinka Margaret Oyebola, Grace Ogunjobi, Egunjobi Motunrayo, Esther Kayode da Peter Anjorin.

Faston ya fashe da kuka yayinda jami'an tsaro suka garzaya da shi gidan yari.

An dage karar zuwa ranar 17 ga Junairu, 2020.

Za ku tuna cewa A ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2019, mutanen unguwa sun bankawa cocin Sotitobire Miracle Centre, dake Akure, birnin jihar Ondo.

Labari ya yadu da safiyar ranar cewa an gano Faston ya birne yaron a mimbarinsa amma da aka isa wajen, sai aka samu cewa ba gaskiya bane.

Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce abinda ya basu mamaki shine yan sanda suna kokarin hana mutane shiga cocin inda suka bazama cin zarafin mutane, suna fitittikarsu daga cocin. Hakan yasa suka banka wuta.

Akalla mutane 3 da dan sanda daya sun rasa rayukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel