Manyan Najeriya na fada da Buhari ne ba don komai ba sai don rijiyar mai – Garba Shehu

Manyan Najeriya na fada da Buhari ne ba don komai ba sai don rijiyar mai – Garba Shehu

Fadar gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa wasu manyan mutane a Najeriya na yaki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba don komai ba sai don kawai ya hanasu lasisin mallakar rijiyoyin mai.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a Villa, inda yace suna sane da takun da manya a Najeriya suke yi, kuma walki suke daidai da kugun kowa.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kaddamar da hari a jahar Neja, sun halaka mutane 8

Da yake magana a kan mutanen da ake zargi da zagaye shugaban kasa, Malam Garba yace babu wata gwamnati da aka taba yi da bata da amintattu, sai dai mu a Najeriya sai a ke amfani da Kalmar ‘Cabal’ domin a bata musu suna.

“Duk wani shugaban kasa yana da mutanen dake bashi shawara, ba laif bane don ka zabi wasu zababbun daka amince dasu, yawancin wadanda suke tare da shugaba Buhari mutane da suka kafu, sun samu nasara a rayuwa, basu da bukatar zama a gwamnati, toh amma saboda su bauta ma kasarsu yasa suka sadaukar da rayuwansu.” Inji shi.

Haka zalika Malam Garba Shehu ya bayyana damuwarsa game da yadda shafukan sadarwar zamani suka zamto ababen takurawa ga wasu mutane, don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai da ministan watsa labaru domin kawo karshen matsalar.

A wani labarin kuma, Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana ma magoya bayansa cewa ba su zabe shi domin ya dinga rikici da bangaren zartarwa ba, amma dole ne idan ta kama zasu iya samun sabani da juna.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba a yayin taron karshen shekara inda yake raba ma jama’ansa alheri a jahar Legas, inda yace don kawai suna samun fahimtar juna da bangaren zartarwa hakan bai sa sun zama yan amshin shata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel