Innalillahi wa Innailaihi raji’un: Sarkin Yakin Kazaure, Baba Santali ya rasu

Innalillahi wa Innailaihi raji’un: Sarkin Yakin Kazaure, Baba Santali ya rasu

Tsohon kwamishinan ayyuka a jahar Jigawa, hamshakin dan siyasa, fitaccen attajiri kuma babban basarake, Sarkin Yakin Kazaure, Injiniya Baba Aliyu Santali ya rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen jahar Kano, Zubairu Mato ne ya tabbatar da haka, inda yace hadarin ya rutsa da Baba Santali ne a kan hanyar Kano zuwa Kaduna a daidai Chiromawa Gadar Kifi cikin karamar hukumar Garun Malam.

KU KARANTA: Ba’a zabe ni kaakakin majalisa don na yi rikici da Buhari ba – Gbajabiamila

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mato ya bayyana cewa wani sundukin kaya da wata babbar mota ta dauko ne ya fado a kan motar Baba Santali, kuma ya dannesu, nan take suka mutu tare da direbansa.

“Mun samu kiraye kiraye daga jama’a game da aukuwar hadarin, ba tare da bata lokaci ba muka garzaya wurin, jim kadan muka kwashe gawarwakin, an samu cunkoson ababen hawa a dalilin wannan hadari, amma dai mun samu nasarar shawo kansa, ba zamu tashi ba har sai mun dauke sundukin daga kan hanya.” Inji shi.

Marigayi Sarkin Yaki sanannen dan siyasa ne a jahar Jigawa wanda ya taba tsayawa takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, amma daga bisani ya fice ya koma APC tare da shuwagabannin PDP na karamar hukumar Kazaure da dubun dubatan magoya bayansa. Da fatan Allah Ya jikanshi da gafara. Amin.

A wani labarin kuma, Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana ma magoya bayansa cewa ba su zabe shi domin ya dinga rikici da bangaren zartarwa ba, amma dole ne idan ta kama zasu iya samun sabani da juna.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba a yayin taron karshen shekara inda yake raba ma jama’ansa alheri a jahar Legas, inda yace don kawai suna samun fahimtar juna da bangaren zartarwa hakan bai sa sun zama yan amshin shata ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel