An yi wa Sojoji 527 horoswa na musamman bayan an yi masu ritaya

An yi wa Sojoji 527 horoswa na musamman bayan an yi masu ritaya

An yi wa Dakarun Sojojin Najeriya 527 ritaya daga aiki. Wadanda abin ya shafa sun hada da Sojojin sama da na ruwa da kuma na kasa.

An yi wa Dakarun horo da ayyukan hannu wanda za su rika yi bayan sun bar aiki.

Daga cikin wanda ritayar ta taba akwai Sojojin kasa 228, da Sojojin ruwa 118, sai kuma jami’ai 181 da ke horas da Sojojin saman Najeriya.

An yi watanni shida ana horas da wadannan tsofaffin jami’ai a hukumar NAFRC na sojojin Najeriya da ke Garin Oshodi a jihar Legas.

Ministan tsaro Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya yi jawabi wajen bikin yaye tsofaffin Dakarun kasar da aka horas bayan yi masu ritaya.

KU KARANTA: Ganduje ya yi kakkaba a Gwamnatin jihar Kano

Magashi ya ba tsofaffin sojojin shawara su dauki matakan gaggawa na ganin ba su burma matslolin da wadanda su ka ajiye aiki su ka saba shiga ba.

Daga cikin cikas din da wadanda su ka yi ritaya su ke samu akwai matsalar rashin kudi, da rashin tattali da kuma larurar rashin lafiya, Inji Ministan.

Har ila yau, Mai girma Ministan ya shaidawa jami’an da su ka bautawa Najeriya cewa gwamnatin Buhari ta na kokarin inganta walwalan jami’an tsaro.

Janar Magashi ya bayyana cewa Najeriya ta ji dadin kokarin da wadannan Dakaru su ka yi wajen ganin an takaita matsalar sha’anin tsaro a lokacinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel