Da zan tona abubuwan dake faruwa a Najeriya babu mai kara yin bacci da ido biyu a rufe

Da zan tona abubuwan dake faruwa a Najeriya babu mai kara yin bacci da ido biyu a rufe

Tsohon ministan tsaro na kasa, Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya), ya bayyana cewa da zai tona asirin abubuwan dake faruwa a cikin kasa, 'yan Najeriya zasu daina yin bacci cikin kwanciyar hankali.

Tsohon ministan, wanda aka fi kira da "TY Danjuma", ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi da kuma bayar da kyaututtuka da jaridar Tribune ta shirya.

"Babu wani sauran me katabus a cikin manyan 'yan kabilar Yoruba saboda a tsorace suke yayin da sauran jama'a ke cigaba da nuna halin 'ko in kula' a kan abun dake faruwa. Da zan fada muku abunda na san yana faruwa a Najeriya a yanzu, zaku daina bacci."

"Zan yi amfani da gargadin dattijo, Cif Adebanjo, a saboda haka, mai son samun cikakken bayani, sai ya same ni a gefe," a cewar TY Danjuma.

Sannan ya cigaba da cewa, "Mun fada cikin wani wawakeken rami a matsayinmu na kasa. Kuma har yanzu mutanen da suka wulla mu cikin wannan rami, sune ke cigaba da mulkinmu a yau. Ya kamata mu farka. Mune kadai zamu iya ceton kanmu duk da kasancewar muna addu'ar Allah ya cece mu."

Kafin kalaman tsohon ministan, shugaban kungiyar "Afenifere" ta 'yan kabilar Yoruba, Cif Bayo Adebanjo, ya ce yankinsu yana cikin garari tare da bayyana cewa, "an danne mu."

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tana kokarin rufe bakin 'yan kabilar Yoruba ta hanyar dakushe muryar gwamnonin yankin dake fafutikar kwatar wa yankin hakkinsa.

'Yan kabilar Yoruba sun shiga damuwa ne biyo bayan kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, da wasu manyan 'yan siyasar arewa a jam'iyyar APC, a kan cewa ba arewa ba zata mika mulki ga kowanne yanki na kasa ba bayan karewar wa'adin shugaba Buhari a shekarar 2023.

Bangaranci, addini, da kabilanci suna taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, lamarin da yasa jam'iyyu suka rungumi tsarin karba - karba a tsakanin bagaren arewa da na kudu da kuma hada Musulmi da Kirista a takarar kujerar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel