Tirkashi: Budurwa ta cirewa saurayinta harshe ficik a yayin da suke sumbatar juna

Tirkashi: Budurwa ta cirewa saurayinta harshe ficik a yayin da suke sumbatar juna

- Wasu hukumomin tsaro na kasar Kenya na neman wata budurwa ido rufe bayan da ta tsinke harshen saurayinta

- Budurwar mai shekaru 23 ta tsinke harshen saurayin nata ne yayin da suke sumbatar juna a wata masahaya

- Ganau ba jiyau, sun ce basu san dalilinta na yin hakan ba don an sansu a matsayin tsiffin masoyan juna

A halin yanzu hukumomi sun bazama neman wata mata da ta tsinke harshen saurayinta bayan da suke sumbatar juna.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, matar da ba a gano ta ba har yanzu, na da shekaru 23 a duniya. Ta tsinke harshen saurayin nata ne a wata mashaya dake Naivasha, a kasar Kenya. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar inda ta tsinke harshen tare da tofar dashi a kasa sannan ta tsere.

Har yanzu dai ba a san dalilin da yasa budurwar ta yiwa saurayin nata haka ba, in ji shaidu.

“Su biyun sun kasance suna ta shan giyarsu a lokacin da mutumin ya fara sumbatar matar. Amma babu wanda ya san dalilinta na juya msihi baya,” in ji Francis Wahome, wanda ya ke wajen yayin da abun ya faru.

“Bayan ta cijeshi tare da tsinke mishi harshe, matar ta gudu inda ta bar mutumin cikin tsananin radadin ciwo. A nan ne aka kwasheshi sai asibiti,” in ji shi.

KU KARANTA: Bakin kishi yasa na kashe'yar gidan kishiyata - Aisha Abubakar

Wahome ya bayyana cewa, ba zasu iya kintatar abinda yasa ta hari mutumin ba. Ya ce an sansu tuntuni a matsayin masoyan juna kuma suna kai ziyara akai-akai zuwa mashayar.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban ‘yan sandan yankin, Hassan Guyo ya ce ana cigaba da neman wacce ake zargin, kuma mutumin na cigaba da samun sauki.

“Mutumin baya iya magana saboda babban kaso na harshenshi baya cikin bakinshi. Wacce ake zargi da aikata hakan kuma ta yi layar zana,” Guyo ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel