Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a gwamnatin Matawalle, kwamishanoni biyu sun yi murabus

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a gwamnatin Matawalle, kwamishanoni biyu sun yi murabus

Da alamun akwai rashin jituwa a gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Muhammad Bello Matawalle, yayinda kwamishanoni biyu da mai bada shawara daya sunyi murabus makonni biyu bayan rantsar da su.

Kwamishanonin sune na Ilimi, Alhaji Jamilu Zanna, da Bilyaminu Shinkafi na ma'aikatar ilimin gaba da sakandare.

Hakazalika, dan uwan, Alhaji Kabiru Marafa, tsohon dan takaran gwamnan jihar, Alhaji Sambo Marafa, ya yi murabus daga matsayinsa na mai baiwa gwamna shawara kan farfado arzikin noma.

Daya daga cikin kwamishanonin da sukayi murabus, Jamilu Zanna, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Ba na jin dadin yadda ake gudanar da wannan gwamnati. Ban gamsu da yadda abubuwa ke tafiya ba."

"Wani dalilin da yasa nayi murabus shine, lokacin da nayi rashin lafiya na tafi kasar Indiya jinya, na kwashe kwanaki arba'in amma gwamnan bai kirani a waya ba domin sanin yadda nake. Saboda haka ba zan iya aiki a gwamnatinsa ba."

Ya kara da cewa a matsayinsa da shugaban kwamitin kamfen Matawalle, babu mambobinsa da aka baiwa wani mukami, saboda haka, ba ya bukatar kujera a majalisar gwamnan saboda gudun gobe.

Shi kuma Bilyaminu Shinkafi ya yi murabus ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya nadashi matsayin mamban ma'aikatar majalisar dokokin tarayya.

Shi kuma Marafa ya ce yayi murabus ne saboda ya mayar da hankali kan kasuwancinsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel